Yadda Aka Gudanar Da Bikin Maulidin Bana A Ghana

Taron Maulid

Musulmi a birnin Kumasin Ghana sun bi sahun miliyoyin takwarorinsu a fadin duniya suka gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) a ranar Asabar 8 watan Oktoba 2022.

A duk shekara, ana gudanar da bikin ne a ranar 12 ga watan Rabiul Awal, wata na uku a kalandar Musulunci.

Wannan shi ne karo na 78 da aka gudanar da wannan maulidin da Sheikh Ahmed Babalwaiz ya assasa a birnin Kumasi.

Kamar yadda yake a fadin duniya, idan wannan rana ta zagayo, mafi yawancin kasashen duniya suna ba da hutu ga al’ummar Musulmi domin su ji dadin gudanar da bukukuwan Maulidin Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Taron Maulid

Domin haka ne maga kujerar taron, Sheikh Mustapha Ibrahim ya yi kira ga gwamnati, a madadin musulman Ghana, da ta kara rana irin ta yau, a cikin ranakun hutu na kasa.

Ya ce "idan duk duniya na amfana da wannan ranar, me zai hana mu ma ‘yan Ghana mu amfana da ranar wannan bukin”.

Taron Maulid

Babban bako mai jawabi, Imam Mohammed Masrur Ibrahim, Limami a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya, ya yi jawabi ne a kan taken taron Maulidin, “Kin ta’adanci a koyarwar musulunci”.

Bayan ya yi bayanin ababan da suke sa mutum ya kasance dan ta’adda guda uku; wato neman suna, yunwa da rashin aminci, da kuma wuce gona da iri ko tsaurin ra’ayi, sai ya kawo kadan daga cikin yadda za a magance ta’adancin.

Yce, samarwa matasa aikin yi, amfani da ‘yan sandan sa kai na unguwanni da kuma wayar da kan musulmai cewa.

“Musulunci bai ce mu yi ta’addanci ba. Musulunci ba ya koya maka ka je ka cuci wani sai dai akasin haka.”

Taron Maulid

Ben Abdallah Banda, kodinetan ci gaban Zanguna da tsakiyar birni, wanda ya zo a madadin mataimakin shugaban kasa ya yi kira ga musulmi da su kwaikwayi Annabi Muhammad (SAW), kamar yadda ya yi hijira zuwa Madina a lokacin da ake nunawa Musulunci kiyayya, maimakon ya yake su a Makka.

Mun nemi jin daga wakilin gwamnati, Ben Abdallah Banda, game da kira da maga kujeran taro ya yi na kara rana irin ta yau a cikin ranakun hutu na kasa a hukumance, ya ce zai isar da wannan sako ga gwamnati kuma za a bi yadda doka ta gindaya wajen tabbatar hakan.

Saurare rahoton Idris Abdullah a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

GHANA: Yadda Musulman Kumasi Suka Gudanar da Bukin Maulidin Bana