Yadda Musulmai Ke Taya Kiristoci Bikin Kirsimeti A Ghana

Yadda A Ghana Kristoci Da Musulmai Ke Shirin Gudanar Da Bikin Kristimeti Cikin Kwanciyar Hankali

Yayin da ake yawan samun aukuwar rikice-rikice na addini ko banbance-banbancen ra'ayi a wasu ƙasashe, a Ghana, lamarin ya sha banban, saboda Musulmai da Kirista kan taya junansu murna a lokacin manyan bukukuwan addinan biyu.

ACCRA, GHANA - Hakan ya bayyana a fili saboda zaman lafiya da kwanciyar hankali da kasar Ghana ke gani a duk lokacin bukukuwan manyan addinai guda biyu kamar bikin Kirsimeti da na Idi babba ko karama, Musulmai da Kirista suna haduwa domin yin bukukkuwar tare.

Yadda A Ghana Kristoci Da Musulmai Ke Shirin Gudanar Da Bikin Kristimeti Cikin Kwanciyar Hankali

Babban abin da ya fi daukan hankali kuma shi ne kasancewa Musulmi ba sa cin yankan wadanda ba Musulmi ba kamar yadda addini ya bayyana, wasu Kiristocin a Ghana suna gayyatar Musulmai da su yi musu yankan dabbobin su a lokacin bukukuwar Kirsitmeti saboda idan sun ba su abincin za su iya ci.

Yadda A Ghana Kristoci Da Musulmai Ke Shirin Gudanar Da Bikin Kristimeti Cikin Kwanciyar Hankali

Kwaku dan cocin Presbyterian Ghana ya ce suna gayyatan Musulmai a ranar 31st ga watan Disamba wato 31st night ko wace shekara kuma Musulmi ke musu yanka.

Pasta Fillix na cocin Author of Fire a birnin Accra ya ce, Kiristocin Ghana da Musulmi na zaman lafiya, kuma akwai fahimtar juna babu tashin hankali tsakaninsu.

Yadda A Ghana Kristoci Da Musulmai Ke Shirin Gudanar Da Bikin Kristimeti Cikin Kwanciyar Hankali

Mallam Rabiu Maude dan Masanin birnin Accra ya ce yana da kyau sauran kasashe musamman kasashen Afirka su yi koyi da Ghana.

Mafi girman addini da yawan mabiya a Ghana shi ne addinin Kirista wadanda ke da kaso 71.2 %.

Saurari cikakken rahoto daga Hawawu AbduKarim:

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Musulmai Ke Taya Kiristoci Bikin Kirsimeti A Ghana