Yadda a Aka Yi Bukukuwan Kirsimeti a Najeriya

Babban birnin tarayyar Najeriya Abuja ya samu raguwar cunkoson motoci a daidai lokacin da ma'aikata da sauran jama'a ke tafiya garuruwansu don bikin Kirsimeti, da kuma masu tafiya hutun karshen shekarar.

Duk da haka, an kayata garin da ado irin na zamani har ma da wasu furanni kasancewar bikin Kirsimeti.

Kama daga hedikwatar 'yan sanda da ke kusa da fadar shugaban kasa ta Aso Rock, zuwa kamfanin man fetur da ke sashin tsakiyar birnin, duk an kayata su da kwayayen wuta masu walkiya.

Tashoshin mota kuma na cike da fasinjoji da kan tafi garuruwansu na asali don sufurin jirgin kasa yana zuwa Abuja da Kaduna ne kadai.

A tashar motar Maraba da ke jihar Nassarawa daf da Abuja matafiya sun bayyana wa Muryar Amurka yadda su ke ji a ransu a wannan lokaci.

Akwai kuma, wadanda aka zanta da su, da za su yi bikin a Abuja, inda su ka fi maida hankali ga nau'o'in abinci da za su dafa. 'Yan kasuwa na baje hajarsu kamar kayan abinci da na tufafi.

Abdullahi Magaji mai sayar da kayan miya da na lambu, ya fadi yadda farashi ya ke a wannan lokaci.

Gwamnatin Najeriya ta ba da hutu a ranakun Laraba da Alhamis domin bukin kirsimeti, inda kuma ta ayyana Laraba ta makon gobe a matsayin ranar hutun sabuwar shekara ta 2020.

A saurari rohoto cikin sauti daga wakiliyar Muryar Amurka Hauwa Umar.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Najeriya Ta Bi Sahun Kasashen Duniya Wajen Yin Bukukuwan Kirsimeti