An bukaci matasa dasu taimakama kawunansu da kansu domin kasancewa masu dogaro da kai wata matashiyar ‘yan kasuwa Malama Hauwa Mahmoud Wali, ce ta furta haka a zantawarsu da wakiliyar Dandalinvoa Baraka Bashir, a birnin Kano.
Matashiyar ta ce sana’ar hannun na da alfanu domin a cewarta da sana’ar ta mallaki gidaje da filaye har da shaguna guda biyu baya ga wasu harkokin da take yi a gida.
Malama Hauwa ta bayyanawa wakiliyar DandalinVOA cewa kimanin shekaru 7 kenan da ta fara wannan sana’ar kuma da taimakon Allah ta ga fa’idar sana’ar dogaro da kai.
Ta ce kawo yanzu tana da kimanin ma’aikata guda talatin da ke cin abinci a karkashinta, inda ta ke cewa ta fara sana’ar ne da kadan-kadan inda daga bisani ya habbaka har ta kai ta inda take a yanzu.
Ta ce tana sayar da kayan mata, zanin gada,takalma da su turaruka kuma ta ce tana fita kasashe domin saro kayayyaki.
Hauwa ta ce ta kan je Togo, Cotonou, Algeria da Niger da makwatan kasashen domin saro kayayyaki, kuma babban abinda ke ci mata turo a kwarya ba bai wuce, matsalolin takarda neman izinin shiga musammam ma a kashen Faransawa.
Ta kara da cewa da kanta ta ke zuwa wadannan kasahe domin saro kaya, ta ce wahalar hanyar zuwa kadai aiki ne
Ka wo yanzu ta ce babban burin ta bai wuce ta gina makarantar Islamiyya domin su sami ilimi.
Your browser doesn’t support HTML5