Kamar yadda muka alkawarta wa mai sauraro mun dora a hirarmu da mawaki Umar Ayuba Isah wanda aka fi sani da Dabo the prof, Mr lada goma, wanda ya ce baban fatansa wakokinsa su shiga lunguna da sakuna tare da isar da gamsassun bayanai.
Ya ce daga cikin baiwarsa yakan yi amfani da kida da wasu harsunan don rera wakokinsa tare sauraran wasu kalmomi da kuma sauya baituka ko canza su cikin nasa harshen.
Mr lada goma ya ce fatansa ba wai ya tara dukiya ba, burinsa kawai ya bar baya ana kwatance da shi, ya kuma kara da cewa kamar kowanne mawaki shima yana da tasa matsala mussaman ma ta rashin tallafa musu tare da damawa da su a harkokin sana’arsu
Daga karshe ya bayyana cewa har yanzu ana da karanci wayewa wajen amfani da kafofin sadarwa ga mawaka masu tasowa.
Facebook Forum