Rundunar ‘yan Sandan jihar Legas ta chafke wani mutum mai suna Kingsley Oriaku mai shekaru 37 wanda ya siyar da ‘yar shi da ‘yar makwabcin shi a wani gidan marayu na karya.
Wanda ake zargin ya siyar da ‘yarshi Nkechi mai shekara daya da dan makwabcinsa mai shekara bakwai akan kudi Naira dubu 120 domin ya binne surikar shi.
Kwamishinan ‘yan Sandan Legas CP Edgl Imohimi ya gurfanar da Oreiaku inda ya amsa laifinshi na saida yaran saboda bakin ciki da rudani da kuma bukatar kudi domin binne surikar tashi.
Yace “nasan abinda nayi ba daidai bane amma ina cikin damuwa”
Ya kara da cewa matarsa ita kadai ce iyayenta suka haifa da surikat ta mutu a watan Satumba sai sauran dangin suka bace lissafin adadin kudaden da ake bukata na fitar hankali, kuma shi bai san abin yi ba shine ya dauki ‘yar su ya mikata zuwa ga mai gidan marayun, wacce ya san ta hanyar abokanai, kuma tace tana siyan yaran da basuda iyaye, sai na tuna ta a lokacin da nake tsananin bukatar kudi.
Sai daga baya muka fara samun matsala da matata da ta gane cewa na siyar da yarinyar sai ta kaini wajen ‘yan Sanda , da mukaje na amsa laifina kuma muka sasanta.
Bayan kwana biyu sai ya yaudari dan makwabcinsa mai suna Gabriel, da alawa yasa ya bishi waje, suka nufi tashar mota inda suka hau motar dare zuwa Aba. Ya kuma kira me gidan marayun kafin na bar Legas, ta amince akan zata bashi Naira dubu 190 amma da suka isa sai tace dubu 120 kawai gareta.”