Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro mai barin gado, Jake Sullivan, ya yi kira ga gwamnatin Trump mai shigowa, da ta ci gaba da dabarun Shugaba Joe Biden na karfafa dangantaka da abokantaka da kawayen Indo-Pacific, domin kalubalantar abokan hamayya, ciki har da China da Koriya ta Arewa.
"Batun da za mu yi musu shi ne cewa, matsayin Amurka a yankin na da matukar karfi a yanzu," in ji Sullivan, a yayin da yake amsa tambayar Muryar Amurka a wani taron tattaunawa da 'yan jarida a jiya Juma'a.
Ya ci gaba da cewa “ya kamata a sami ci gaba fiye da gagarumin sauyi dangane da dabarunmu na Indo-Pacific, amma ba mu san abin da gwamnati mai shigowa za ta yi ba."
Sullivan, wanda ke bayyana daya daga cikin manyan tsare-tsaren gwamnatin Biden na yankin Indo-Pacific, ya ce tsarin shugaban yana "aiki matuka," kuma ya yi gargadin cewa kaucewa daga hakan "babbar kasada" ce.
Duk da haka Sullivan ya yarda cewa gwamnatin ta kasa samun ci gaba na a zo a gani, kan kawar da makaman nukiliyar Koriya.
Yayin da barazanar Pyongyang ta ci gaba da tsananta fiye da ko wane lokaci, Sullivan ya nuna wasu mahimman muhimman batutuwa: haɗin gwiwa tsakanin Koriya ta Arewa da Rasha, da kuma "babban kawancen abokan hamayya, wato Rasha, China, Koriya ta Arewa, da Iran."
Ya sake nanata gargadin da gwamnatin kasar ta yi game da rage tallafin da Amurka ke baiwa Kyiv, wani abu da zababben shugaban kasar Donald Trump ya bayyana cewa zai yi.
Sullivan ya ce abin da ke faruwa a Ukraine yana da matukar muhimmanci ga yankin Indo-Pacific, saboda "China na zuba ido."