ABUJA, NIGERIA - Maryam Nyako matashiya ce ‘yar Najeriya, ta ce fada a kan ‘yan siyasa bai da fa’ida, saboda kusan duk kansu a hade yake.
A wata hira ta musamman da muryar Amurka a birnin tarayya Abuja, tsohon dan majalisar tarayya kuma babban manomi daga jihar Jigawa honarabul Faruk Adamu Aliyu, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su koya wa ‘yan siyasar kasar hankali su daina barin fadan masu ruwa da tsaki daga sama ya rika shafar su.
A wani bangare kuwa, a yayin sharhi kan babban zaben shekarar 2023 da ke gabatowa, mataimakin dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar AAC, Barista Haruna Magashi, ya ce lokaci ya yi da ‘yan Najeriya zasu nuna cewa katin zabensu da kada kuri’a su ne makamin su.
Ita ma Malama Fatima Hamza ta ce cancanta ya kamata ‘yan Najeriya su rika bi wajen zaben shuwagabanni ba jam’iyya ba.
Za a iya cewa zuwa yanzu, magoya bayan ‘yan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyu kamar su APC, PDP, Labour da NNPP sun fara farfaganda tsakanin juna a game da tallata ‘yan takarar da suke mara wa baya, lamarın da masana siyasa ke ganin kara fadakar da jama’a kan muhimmancin zaben wadanda suka cancanta shi ne mafi a’ala.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5