Ya Kamata Gwamnatin Najeriya Ta Bayyana Yadda Ta Ke Sarrafa Kudadden Sata Da Ta Kwato - Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar III

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar na III, ya kalubalanci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta yi cikakken bayanin akan yadda za ta yi amfani da kudaden satar da ta kwato, da abin da za’a yi da kudadden da kuma inda suke a halin yanzu.

A yayin da yake jawabi ta bakin Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaidu a taron tattaunawar masu ruwa da tsaki kan manufofin da’a na kasa, wanda ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya shirya, tare da hadin gwiwar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC a shiyyar Arewa maso yamma, Sarkin Musulmi ya ce 'yan najeriya na bukace da sanin adadin kudaden da aka kwato, dakuma yadda ake sarrafa su.

Mai alfarma Sarkin Musulmi ya ce yin wannan bayani ya zama wajibi, musamman la’akari da yadda bangaren ilimi da saura bangarori kamar tituna da asibitoci su ke matukar bukatar kulawar gwamnati.

Ya bayyana cewa rashin yin bayani mai gamsarwa game da dukiyoyin da gwamnatin tarayya ke cewa tana kwatowa daga hannun tsofafffin shugabannin da suka yi rub da ciki da kudadden jama’a, kan iya haifar da shakku a zukatan 'yan kasa, wasu lokuta ma har da matsalolin da ba'a zata ba sakamakon matsin da ‘yan kasar ke cici ta fuskar tattalin arziki.

Haka kuma, Sarkin Musulmi ya ce a baya-bayan nan majalisarsa ta wallafa litattafai da dama a kan munin cin hanci da rashawa da kuma ba da shawarwari kan yadda za'a magance matsalar.

Akan haka yayi kira ga ’yan kasa da su nemi litattafan domin samun ilimin magance matsalar cin hanci da ta yi wa Najeriya katutu.

A na sa bangare, shugaban hukumar ICPC mai kula da jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara, Ibrahim Alkali, ya ce bullo da manufofin da’a na kasa ya zama wajibi a tafarkin yaki da cin hanci da rashawa.

Alkali ya ce ana kuma aiwatar da su ne da nufin maido da nagarta da rikon amana da suka yi karanci a kasar a halin da ake ciki yanzu.

Idan za'a iya tunawa, a baya-bayan nan gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta yi nasarar dawo da wasu makudan kudadden da wasu dangin tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori ya wawure a lokacin da ya ke kan karagar mulki, da suka kai fam miliyan 4.2 lamarin da ya jawo muhawara kan wa ya kamata ya karbi kudin.