Tun lokacin da matsalar rashin tsaro ta soma yin kamari a Najeriya gwamnatoci ke ta kashe makudan kudade wajen kawo karshen matsalolin.
Alal misali, an sawo jiragen yaki, motocin aiki ga jami'an tsaro, makamai tare da tura jami'an a sassan da ke da matsalolin da sauran matakan da aka dauka, amma har yanzu kamar ana kara rura wutar matsalolin ne.
Gwamnan Sokoto dake arewa maso yammacin kasar Aminu Waziri Tambuwal wanda cikin wannan mako ya gana da shugaban Najeriya akan matsalolin rashin tsaro dake haddabar jiharsa, yana ganin da gwamnatin Najeriya za ta yi amfani da mutanen yankunan da ke fama da matsalolin ta kafa rundunar tsaro ta musamman da watakila an samu bakin zaren warware matsalolin.
Dama masana tsaro sun jima suna bayar da irin wannan shawara ta a samar da jami'an daji da suka kira ‘Forest Marshall’ a turanci kamar yadda shugaban sashen nazarin laifuka da samar da tsaro na jami'ar Yusuf maitama Sule da ke kano Detective Auwal Bala Durumin Iya ya jima yana fada.
Wani abu dake ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya shi ne yadda ake ci gaba da samun koma bayan lamurra, abin da gwamna Tambuwal ya ce yana mai ra'ayin a sake fasalin kasa, inda ya bayar da misali da yunkurin gyaran tsarin mulkin kasar da suka yi lokacin da yake kakakin majalisar wakilai.
Ya kara buga misali da samar da wutar lantarki a jihohi ba tare da alaka da gwamnatin tarayya ba, da samar da ‘yan sandan jihohi, da makamantan su.
Duk wadannan shawarwarin dai masu bayar da su, suna fatar ganin an samu daidaituwar lamurra ne a Najeriya, kuma gwada amfani da su ne kadai kan iya nuna tasirin su ko akasin haka.
Sauraro cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5