Ya Ake Ciki Game Da Yarjejeniyar Amurka Da Taliban?

Babban kwamandan dakarun Amurka a Afghanistan ya ce, Amurka ba ta da niyyar ta yi watsi da matsayar da aka cimma da Taliban, amma akwai alamu da ke nuna cewa, wannan yarjejeniya da aka kulla ba za ta kai labari ba.

Janar Kenneth McKenzie ya ce, an samu raguwar tashe-tashen hankulan da ake gani, amma hare-haren da kungiyar ta Taliban ke kai wa babu kakkautawa na ci gaba da zama abin damuwa.

Ita dai wannan matsaya da aka cimma tsakanin Amurka da Taliban a birnin Doha na kasar Qatar a watan Fabrairun da ya gabata, ta nemi dakarun Amurka da sauran na hadin gwiwa su fice daga kasar cikin watanni 14 masu zuwa.

Jami’an sojin Amurka dai sun ce a wannan mako sun fara janye sojojinsu.

Baya ga yawan kai hare-hare, wani batu da wasu ke ganin zai iya zama cikas ga matsayar da aka cimma, shi ne, watsi da kungiyar ta Taliban ta yi da wani umurnin da gwamnatin Afghanistan ta bayar, na sakin fursunonin kungiyar bisa wasu sharudda da aka gindayawa mayakan na Taliban.