A cikin sabon shirin namu na Bana- Bakwai, mun zanta ne da matashi mai suna Mai Nasara Nasarawa Funtua, dake jahar katsina, da kuma inda suka bayyana mana manufar wasu sababbin kalmomi da matasa ke anfani da su.
Mainasa daga garin Funtua ya ce idan kaji matashi ya ce " Ɗan Laushi " yana nufin wani mashinne na roba mai taushin kara kuma duk matashin da aka gani akan sa, yana nufin matashin ya hadu kenan.
Shi kuma Abbas Baffa Cheledi daga jahar Bauchin Najeriya cewa yayi idan kaji matashi ya ce "Baba ya zamu hau sama ne?" wanan kalami na nufin yau zamu fita fira wurin budurwa ko kuma majalisa kenan!,
Haka kuma idan kaji matashi ya ce "Baba wannan yaron ya raina ni fa, abokin na iya ce wa to BASHI RUWA MANA. Wannan yana nufin ka bashi kashi kenan.
Mu hadu a shafin mu na dandalinvoa/facook.com domin jin irin naku sababbin kalmomin.
Saurari Karin bayani.