Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Karrama Musulunci a Birnin New York


Sallah a Amurka
Sallah a Amurka

Yau take sallah a fadin duniya. Kimanin yara ‘yan makarantar firamari da sakandire milliyan daya da dugo daya 1.1 za su bi sahun sauran yara a duniya, don bukin sallah babba.

Garin New York shine gari mafi girma a duniya, wanda ya hada mutane, da ban da ban na duniya, hakan yasa milliyoyin musulmai da suke a garin, sukayi yakin neman a baiwa ‘ya'yan su hutu a duk ranar sallah karama da babba.

A ‘yan watannin baya ne shugaban karamar hukumar garin New York, ya amsa wannan rokon na mutanen garin. Yau a karon na biyu yara ‘yan makarata, sun samu zuwa masallacin Idi tare da iyayen su.

Kimanin makarantu dubu daya da dari takwas ne 1,800 a cikin garin New York ake hutu a yau, yara da malamai ba za su je aiki ba, don bukin sallah babba, wanda idan Allah ya kaimu gobe, akwai hutu shima wanda yayi dai-dai da hutun “Yom Kippur” na mabiya addinin Yahudu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG