Yayin da sama da jami’an kashe gobara dubu 12 ke ta kokarin shawo kan wata wutar daji da ke ci a California da ke Amurka, gwamnan jihar Gavin Newsom ya ce, ya nemi taimakon kasashen Canada da Australia, baya ga tallafin da ya nema daga gwamnatin tarayya.
Gwamnan ya ce Australia na daya daga cikin kasashen da ke da “kwararrun jami’an kashe wutar daji a duniya.”
A ranar Juma’a Newsom ya ce, wutar dajin ta yi ta’adi matuka a arewacin jihar, inda dubban mutane suka tserewa gidajensu kana wasu daruruwan gidaje da gine-gine suka kone.
A cewar Newsome, “an kwashe shekaru da dama rabon da jihar ta ga irin wannan wutar daji,” yana mai cewa wutar tana karar da kudade da kayayyakin da ke hannunsu.
Akalla mutum biyar ne suka mutu kana wasu 43 suka jikkata ciki har da jami’an kashe gobara, a wannan wutar daji, da ta lakume yankin da nisansa ya kai kilomita dubu 2,020.