Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya reshsn jihar Adamawa Bishop Mike Moses ya furta hakan a yayin kammala addu'o'i na musamman da kungiyar ke gudanarwa shekara shekara.
Bishop Mike Moses yace suna kiran gwamnatin jihar Adamawa da gwamnatin tarayyar Najeriya yace su taimaka a sake gina mijami'un da aka kona a kananan hukumomi bakwai kuma mutanen dake gudun hijira da sun fara komawa wurarensu. Yace mutanen suna shan wahala. Babban kiran da yake yi shi ne idan an taimaka masu an sake gina masu wuraren ibada tunanensu kan abun da suka fada ciki zai ragu.
Daya daga cikin dattawan kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jihar Adamawa Saleh Kingir ya bayyana mahimmancin taron dake zuwa daidai lokacin da kiristoci ke tunawa da tashin Isa Almasihu daga mutuwa. Yace tashin Isa Almasihu daga matattu ya ba kirista iko kan mutuwa ya kuma bada begen shiga mulkin Ubangiji.
Shi ma shugaban kungiyar kirista ta Najeriya reshen karamar hukumar Yola ta Arewa Pastor Icem Sule ya kalubalanci kiristoci su sadakar da kai wajen gudanar da addu'o'i da azumi domin hadin kai da zaman lafiya domin gina kasar Najeriya.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5