Jami’an Falasdinu sun ce wani farmakin Isra’ila a arewacin Gaza ya kashe akalla mutane 22 da galibin su mata da yara ne. Hare haren da Isra’ila ta kai yankin da aka daidaita sannan mutane sukakaurace mishi ya shiga mako na 3 yau Lahadi yayin da kungiyoyin bada agajin jinkai suka bayyana bala'i a game da batun agajin jinkai.
A wani bangaren kuma, likitocin Isra’ila sun ce wata babbar mota tayi karo da wata motar safa a daura da Tel Aviv, wanda yayi sanadiyyar jikkata mutum 35.
Sannan, a gefe guda kuma, shugaban Adninin Iran ya ce “Kada a kururuta ko a sassauta hare haren da Isra’ila ta kai Iran cikin karshen makon nan, yayin da bai yi kira da mai da a da martini ba, lamarin da ake ganin yana nufin cewa Iran tana auna matakin da zata dauka nan gaba cikin tsanaki.
A ranar Asabar ne, jiragen yakin Isra’ila sun kai hari cikin Iran a matsayin harin gayya na harin makaman mizile din da Iran ta kai mata a farkon wannan watan na Oktoba.