Hukumar lafiya ta duniya ta WHO za ta tura wata tawagar kwararru na kasa da kasa China a wannan makon don binciken yadda cutar coronavirus ta samo asali.
WASHINGTON, D.C. —
Ko da ya ke, nan take dai ba a san ko za a bar kwararrun, da aka shirya zasu yi tafiyar ranar Alhamis zuwa birnin Wuhan ba da ke tsakiyar China, inda cutar ta fara bulla a shekarar 2019.
“Ya na da muhimmanci tun da hukumar ta WHO ce ke jagorantar yaki da annobar, ta kuma kasance mai jagorantar kokarin gano yadda cutar ra samo asali ta yadda zamu shirya sosai, abinda mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric ya fada kenan game da tawagar da zata China.
Sanarwar da China ta fidda yau Litinin akan zuwan kwararrun na hukumar WHO kasar na zuwa ne yayin da kasar ta bada rahoton samun mutun 103 da suka kamu da cutar COVID-19, adadi mafi yawa da kasar ta gani cikin sama da wata 5.