WASHINGTON D.C. —
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce karuwar wadanda suka harbu da COVID-19 a baya-bayan nan a Beijing da aka gani, alama ce da ke ya nuna cewa ko wuraren da suka yi nasarar shawo kan cutar ka iya fuskantar sabuwar barazanar barkewar cutar.
A yayin jawabin da ya saba yi wa manema labarai, a jiya Litinin, Sakatare Janar na WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce Beijing ta shafe kwanaki 50 ba tare da ta ba da rahoton samun sabbin wadanda suka kamu da cutar ba.
Amma ya ce duk da haka, tun a makon da ya gabata, an tabbatar da cewa an samu sabbin mutum 100 da cutar ta harba.
Tedros ya kuma ce ana bincike kan salin inda cutar ta barke a Beijing, yana mai cewa cutar na ci gaba da karuwa a wasu wurare.