White House: An Tilasta Saka Takunkumi a Bangaren Ofishin Trump

Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce yanzu ana bukatar duk wanda zai shiga bangaren yamma, wanda ake kira West Wing, inda Shugaban kasa kan gudanar da harkokin gwamnatinsa, ya sa takunkumin rufe baki da hanci.

Umurnin na zuwa ne bayan da wasu ma’aikatan fadar ta White House suka kamu da cutar coronavirus a makon jiya.

Wata ‘yar takardar sanarwar da aka aika wa dukkannin ma’aikata jiya Litinin, ta bayyana dalla-dallar sabon salon da aka dauka a bangaren na West Wing, inda ake gudanar da harkokin gwamnatin Shugaba Trump kulluyaumin.

Bisa ga sabon tsarin, an amince ma’aikatan fadar ta White House su cire takunkumin rufe baki da hanci idan suka zauna kan kujerunsu na aiki, kamar yadda wani babban jami’in gwamnati ya fadawa Muryar Amurka kenan.

Manufar tsarin ita ce kare Shugaban kasa Donald Trump, wanda ya yi kememe ya ki sa takunkumin.