Dandalin sada zumunta na whatsapp ya bayyana sababbin tsare tsare ga masu amfani da shi miliyan 200 dake kasar Indiya, biyo bayan yaduwar wadansu bayanai da suka haifar da wata zanga-zanga.
gwamnatin kasar India ta yi barazanar kai kamfanin na whatsapp gaban kotu, inda take cewa " hanyar da akayi amfani da iita wajen yada wadannan bayanai baza ta kaucewa fuskantar hukunci ba." Ma'aikatar yada labarai da sadarwar zamani ta ce " idan suka ci gaba da kasancewa masu sauraro, sun cancanta a hukunta su a matsayin masu tunzura jama'a daga bisani kuma a dauki matakin shari'a a kansu.
Kafar sadarwar, wacce mallakar kamfanin Facebook ce ta ce za ta taikaita damar aika sakonni ga mutane da yawa a lokaci daya ga masu amfani da ita a kasar ta India, inda ta ce mutum zai iya aikawa mutane biyar sako a lokaci daya ne kacal.
Ya kuma kara da cewa zai cire damar aikawa mutane sako kai tsaye daga cikin shafin, kuma anyi hakan ne domin a hana aika sakonni barkatai da suka haifar da zanga zanga.
Kasar India itace tafi kowacce yawan jama'a masu amfani da Whatsapp.
Your browser doesn’t support HTML5