Kafar sadarwar WhatsApp na shirin fitar da wata sabuwar hanya da masu amfani da manhajar za su iya aikawa junansu kudi ta hanyar aika sakon karta kwana.
Wata manhajar WhatsApp da aka kirkira wadda yanzu haka ake gwajinta kuma za a fitar da ita ga wayoyin mutane nan bada dadewa ba, na nuni da cewa za a iya amafani da WhatsApp, wajen aikawa mutane kudi.
Kafar WhatsApp wadda mutane sama da Miliyan, ta fitar da shirin aika kudi daga banki zuwa banki cikin gaggawa, wanda zai yi aiki da babban bankin Indiya. Rahotanni dai sun nuna cewa za a fara gudanar da sabon tsarin a kasar Indiya kafin kowacce kasa.
An shirya kaddamar da gwajin wannan hanya a Indiya, inda WhatsApp, ya dauki kwararru a wannan fannin aiki, zai kuma baiwa kimanin mutane Miliyan 200 damar amfani da app din WhatsApp wajen aika kudi.
Ya zuwa yanzu dai kamfanin WhatsApp yaki ya yi magana ko ya bayar da karin bayani kan wannan sabon tsari.
Kamfanin Facebook wanda shine wanda ya mallaki WhatsApp, yana da irin wannan tsari a manhajarsa ta Messenger app tun shekarar 2015. Shima kamfanin Apple yana aiki kan yadda mutane zasu rika aikawa junansu kudu ta manhajar iMessage app, wadda ake kyautata tsammanin za a kaddamar cikin manhajar iOS 11.
Your browser doesn’t support HTML5