A ranar Talata kunigyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta ayyana Ryan Mayson a matsayin wanda zai horar da ‘yan wasan kungiyar a mataki na wucin gadi har zuwa karshen wannan kakar wasa.
Nadin Mayson na zuwa ne bayan da Tottenham ta kori Jose Mourinho a ranar Litinin, saboda Rashin gamsuwa da irin rawar da yake takawa.
Kwararru, masu sharhi da masoya kwallon kafa sun yi ta hasashen wanda za a nada a matsayin sabon kocin kungiyar.
An yi ta ambato sunayen masu horarwa irinsu Julian Nagelsmann na kasar Jamus, tsohon kocin Juventus Massimiliano Allegri, Brendan Rodgers na Leicester City, Scott Parker na Fulham da dai sauransu.
Amma a karshe, kungiyar ta Tottenham ta tsaya akan Mayson. Shin wane ne Ryan Mayson?
- Shekarar Ryan Mason 29-
- Ya bugawa Tottenham wasa sama da 50
- Ya taba bugawa kungiyar Lorient ta kasar Faransa wasa
- Ya daina buga kwallon ne bayan ya ji mummunan rauni a kansa, bayan gware da suka yi dan wasan Chelsea Gary Cahill.
- A shekarar 2018, ya bayyana cewa ya yi ritaya bayan da likitoci suka gargade shi cewa rayuwarsa za ta iya shiga hadari in ya ci gaba da buga kwallo.
- Daga bisani ya koma makarantar nazarin horar da ‘yan wasa ta Spurs don sanin makamar aikin horarwa.