Rundunar sojin Amurka ta ce ba a sa ran kammala cikakken binciken mummunan harin kwantan baunar nan da aka kai watan jiya a Nijar, har sai watan Janairun badi.
Tawagar masu bincike na sojin, wadda ke karkashin Manjo-janar Roger Cloutier, zai ta tafi wasu wurare a Amurka da Afirka da Turai don ta tattaro bayanan da za su taimaka wajen gano abin da ya faru yayin harin na ranar 4 ga watan Oktoba, bisa ga wani bayani na Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon da aka fitar jiya Laraba.
Jami’an tsaro a Pentagon da kuma Ma’aikatan Tsaron Janhuriyar Nijar sun ce mayakan ISIS ne su ka yi kwantan bauna ma sojojinsu a ranar ta 4 ga watan Oktoba, su ka kashe sojojin Amurka 4 da sojojin Nijar su ma 4 da wani dan Nijar mai tafinta.
Sojojin sun kamalla wata ganawa da shugabannin yankin, sun fara tafiya su shiga motocinsu su koma Kenan, sai kwatsam aka kai masu hari, abin da jami’an Amurka su ka gaya ma Muryar Amurka Kenan.