Wata Yarinya Mai Wanka Da Jinin Alade

Pig farm promotes

Wata matashiya yar shekaru 19 da haihuwa tace wanka da jinin Alade ne yake gyara mata fata, yana kuma ‘kara mata kyau da rashin tsufa.

Yarinyar mai suna Chanel, tayi sunane a wani shiri da ake kira “na damu da zauna a yarinya” da gidan talabishin ‘din Amurka mai suna MTV yake nunawa.

Chanel ta bayyanawa kakar ta dalilin yin wanka da jinin Aladen, inda tace dubunnan shekarun da suka wuce mutane na amfani da wannan hanyar domin kada su tsufa. Shakka tasa kakar ta tace tana son shaida akan mutanen baya sun taba yin hakan, amma Chinel ta kasa bada kwakkwarar shaida.

Tace tana baiwa kakar ta hakuri kan damuwar da take, amma ita fa lokacin wankan ta yayi da jini, kuma ba abinda zai hanata yin wanka da jinin.

Wannan ‘dabi’a dai bata da ma’ana ko tushe, akwai abubuwan da ke gyara fata da jiki wanda suka hada da kula da kyautata tsaftar jiki da cin abinci masu kara lafiya da gina jiki, amma ba wanka da jinin duk wata halitta mai rai ba.