Wata kungiyar gwagwarmaya a Nijeriya ta yi barazana ga gidajen jaridu

  • Ibrahim Garba

Wata kungiyar gwagwarmaya a Nijeriya ta yi barazana ga gidajen jaridu.

Wata kungiyar gwagwarmaya a Nijeriya ta yi barazana ga gidajen jaridun kasar da kuma na kasa da kasa

Wata kungiyar gwagwarmaya a Nijeriya ta yi barazana ga gidajen jaridun kasar da kuma na kasa da kasa, ciki har da Sashen Hausa na Muryar Amurka.

Barazanar na kunshe cikin wata faifan bidiyo mai tsawon minti 18 da aka yada ta kafar “You Tube” a yau Talata da sunan tsattsaurar kungiyar Islamar nan ta Boko Haram.

Hoton bidiyon ya nuna motar da aka dana bama-baman ciki na tarwatsewa ranar Alhamis da ta gabata a harabar ofishin “This Day” wadda daya ce daga cikin manyan jaridun kasar.

Daga bisani, kasidu sun bayyana cewa kungiyar ta yi korafi game da “munanan labarai,” kuma wani mutumin da ba a bayyana sunansa ba, da ya tsaya ganga da wata bindiga, ya yi barazaga ga wasu karin jaridun Nijeriya 7 da kuma Sashen Hausa na Muryar Amurka, da kan yada labaranta ga Nijeriya.

Ba a iya tantance sahihancin hoton bidiyon nan take ba.

A jawabinsa, mai magana da yawun Muryar Amurka, David Borgida, ya ce, “Muryar Amurka ba ta da ta cewa to amman ta na daukar lafiyar wakilanta da muhimmanci.”

Boko Haram, wadda ke kiran kanta Jama’atu Ahlis Sunna Lid Daawati wal Jihad, a baya ta dau alhakin kai hari a Abuja, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 3. Ta kuma dau alhakin kai hari kusa da ofishin “This Day” din na birnin Kaduna, wanda ya hallaka mutane 4.