Hukumomi a yankin Arewa maso gabashin Nigeria sun tabbatar da rahotannin cewa, harin kunar bakin waken da aka auna wani babban jami’in ‘yan sanda ya janyo asarar rayukan mutane akalla biyar. Jami’an suka ce a yau litinin aka kai harin a garin Jalingo, babban birnin jihar taraba, kusa da Ma’aikatar kudi da hedikwatar ‘yan sandan jiha. Amma jami’in ‘yan sandan da aka yi kokarin kashewa ya tsira. An kai wnanan harin ne kuwa kwana guda bayan wani harin da aka kaiwa masu ibada a mujami’ar dake jami’ar Bayero Kano inda akalla sha biyar suka halaka. Jami'an tsaro sunce yan bindigan su jefa nakiyoyi a jami'ar Bayero a jiya Lahadi, sa'anan kuma suka bude wuta akan wadanda ke ibada a yayinda suke rantawa cikin na kare. Manyan Malaman jami'ar guda uku suna daga cikin wadanda aka kashe.
Hukumomi a yankin Arewa maso gabashin Nigeria sun tabbatar da rahotannin cewa an kaiwa wani babban jami’in ‘yan sanda harin kunar baki waken da ya janyo asarar rayukan mutane akalla biyar.