Wata cibiyar bincike dake babban birnin tarayyar Najeriya, wato Abuja ta gudanar da taron yini guda da masu ruwa da tsaki kan harkokin ilimi a jihar Borno kan hanyoyin kare dalibai da malamansu daga firamare zuwa sakandare daga hare-haren kungiyar Boko Haram.
Kungiyar ta gayyato masu fada a ji kan harkokin ilimi da suka hada da malamai da iyaye da masu unguwanni domin fadakar da jama'a kan yadda zasu kare kansu daga hare-haren 'yan ta'adan Boko Haram.
Dr Abiola Akinyode shugabar cibiyar tace ta soma wannan shirin ne tun shekara guda da ta gabata sakamakon wani bincike da suka gudanar inda suka fahimci cewa babu isasshen tsaro a irin makarantun da ake dasu dalili ke nan da ta yunkuro da shirin taimakawa wadannan makarantun.Yakamata su san hanyoyin da zasu kare kansu, su da dalibansu.
Cibiyar tace zata kawo gwamnati cikin shirin. Wadanda suka halarci taron sun bayyana abubuwan da suka koya.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5