Wata Kungiya Mai Zaman Kanta Ta Shigar Da Kara A ECOWAS Game Da Dakatar Da Twitter

ECOWAS

A Najeriya, wata kungiya mai zaman kanta da ake kira 'Love Love Foundation', kuma mai rajin kare hakkin bil adama, ta shigar da kara a kotun ECOWAS inda ta kalubalanci dakatarwar da gwamnatin Najeriya ta yi na ayyukan Twitter a kasar.

Lauyan kungiyar, Samuel Ihensekhien Jr, ya ce matakin kungiyar na zuwa ne bayan da gwamnati a Abuja ta gaza sauya dakatarwar. Wannan ya biyo bayan wa'adin da kungiyar ta ba da na kwana biyu na neman a sauya ya wuce, ranar Lahadi.

Da yake sanar da dakatarwar a makon da ya gabata, Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed, ya ce ana amfani da dandalin sada zumunta ne domin lalata kasar.

A halin yanzu kuwa, manyan wakilai daga kasashen yamma sun nuna rashin jin dadinsu da dakatarwar da aka yi a shafin na Twitter. A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, wakilan sun nuna damuwar cewa haramcin na yin fatali da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya da ke ba da tabbacin fadin albarkacin baki.

Karin bayani akan: ECOWAS, Muryar Amurka, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Kafofin yada labarai na cikin gida sun ruwaito wakilan sun yi wata ganawa a Abuja babban birnin Najeriya Litinin tare da Ministan Harkokin Wajen Geoffrey Onyeama kan matakin da aka dauka a kan Twitter.

Samuel Ihensekhien Jr, lauyan gidauniyar One Love, ya fadawa wakilin Muryar Amurka Peter Clottey cewa hukuncin da gwamnatin Najeriya ta yanke ya sabawa doka kuma an yi shi ne da mummunar akida.

Gidajen Rediyon Najeriya Sun Gana Da Jami'an Diplomasiyya Kan Rikicin Twitter

Your browser doesn’t support HTML5

Gidajen Rediyon Najeriya Sun Gana Da Jami'an Diplomasiyya Kan Rikicin Twitter