Wata Kungiya A Jihar Adamawa Ta Shigar Da Kukanta Ga Majalisar Dinkin Duniya

Taron manema labaran kungiyar Njiya Ngoron

Mazauna yankin Koh mai kunshe da kauyuka goma sha uku karkashin lemar kungiyarsu Njiya Ngoron na karamar hukumar Gerei, sun gabatar da kukan su gaban hukumar kare yancin ‘dan Adam ta Majilisar Dinkin Duniya suna bukatar gwamnatin jihar Adamawa ta biya diyyar naira biliyan biyu.

Wannan na kunshe ne a jawabin Shugaban kungiyar Njiya Ngoron Mr, Masssah Nayangom, na taron manema labarai a cibiyar ‘yan jarida ta kasa a Yola fadar jihar Adamawa, inda ya fito karara yana zargin hukumimin tsaro da gwamnati da cewar suna da hanu a kisan gilla da makiyaya ke yi wa al’umansu tun Ashirin da Hudu ga wata Junairun bana.

Da yake kare martabar rundunarsa, jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sanda na jihar Adamawa DSP Othman Abubakar, yace al’umar Njiya Ngoron ba su yi masu adalci ba domin a sanadiyyar rikicin manoma da Fulani na yankin hukumarsa ta rasa babban jami’inta daya.

Wani mazaunin yankin Eston Titus ya fada a hirar da wakilin Muryar Amurka yayi da shi ta wayar talho, ya nemi bangarorin biyu su kai zuciya nesa kana su ja hankalin jama’arsu kan bukatar zama lafiya da juna.

Wakilinmu Sanusi Adamu ya tambayi Mr, Nayangom ko gaskiya ne Hamma Bachama da Hamma Bata sun tsoma baki da niyyar samo masalaha a rikicin, yace ba su da masaniya kan daukan wannan matakin.

Saurari cikakken rahotan.

Your browser doesn’t support HTML5

Wata Kungiya A Jihar Adamawa Ta Shigar Da Kukanta Ga Majalisar Dinkin Duniya - 2'55"