Hukumar kula da yanayi ta Amurka ta ce, ana ganin za a yi wata iska mai karfi da sanyin safiyar yau Laraba a yankin Los Angeles, lamarin da ke iya haifar da karin kalubale ga ma’aikatan kashe gobara da ke kokarin yaki gobarar dajin da ta kashe akalla mutane 24 sannan wasu 24 suka bace.
Ofishin kula da yanayi a Los Angeles a cikin wani sakon da ya wallafa ta kafar sadarwa ta X " ya ce, har yanzu muna cikin kalubalen tashin wata gobarar saboda haka muna gargadin mutane da su yi taka tsan-tsan a yankunanansu.
Iskar ta kara karuwa ne a kudancin California da safiyar jiya Talata. Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa ta wallafa gargadi akan mummunan yanayin mai cike da hadari, wanda ka iya haifar da "karuwar gobara."
Miliyoyin mutane a fadin yankin sun fuskanci sabon gargadin wutar daji a jiya Talata, yayin da aka dauke wutar lantarki ga dubbun mutane saboda hana layukan wuta tada wata sabuwar gobara.