Wata Cuta Mai Yaduwa Ta Hallaka Mutane 115 A Jihar Katsina

An samu bulluwar wata cuta da ba a tantance ba a wata karamar hukumar jihar Katsina, sai dai bisa ga alamun cutar wasu na alakanta ta da cutar Shawara wato Yellow Fever a turance.

Har zuwa yanzu babu tabbacin alkalumma daga hukumomi dangane da halin da jama’a ke ciki a karamar hukumar Matazu dake jihar Katsina. Wakilin Muryar Amurka ya yi karin haske dangane da halin da ake ciki a yankin. A ‘yan kwanakin nan dai rahotannin na nuna cewar an samu barkewar wata cuta mai alamu irin na cutar shawara ta Yellow Fever a turance.

Ya tabbatar da cewar a ganawar da ya yi da mai anguwa Malam Shu’aibu Iliyasu, wanda ya shaida masa cewar an garzaya asibiti da wasu mutane marasa lafiya, wasu daga cikin su kuwa sun riga mu gidan gaskiya. Alamu na nuna cewar wannan cutar tana yaduwa cikin jama’a, ganin yadda ta yadu cikin al’umma a ‘yan kwanaki kadan, ta kuma yi sanadiyar mutuwar kimanin mutane 115.

Alamun cutar sun hada da zazzabi, ciwon kai, harma ta kan kai ga suma, akwai bukatar mutane su dauki kwararan matakai don rigakafin wannan cutar. Kana da rage yawaitar cudanyya da marasa lafiya. Ya kuma bada shawara cewa a duk lokacin da mutane basa jin dadin jikin su sai su garzaya zuwa asibiti don ganin likita.

Don karin bayani sai a saurari tattaunawar cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Wata Cuta Mai Yaduwa Ta Halaka Mutane 115 A Jihar Katsina