Cibiyar tace gwamnonin jihohin Yobe da Kogi da Zamfara da Ebonyi da Akwa Ibom su ne suka fi kowane gwamna rashin yiwa talakawansu aiki.
Cibiyar tace dukansu babu wanda kwazonsa ya haura kashi 35 cikin 100 na mizamin kidigdiga.
Daraktan cibiyar Farfasa Anthony Kila ya bayyana muradun binciken. Yace binciken zai taimakawa mutane su san menene wadanda suka zaba ke yi masu, zai kuma taimakawa gwamnonin su kara kwazo. Binciken zai taimakawa tarihi domin a san abun da ya faru a baya.
Kwamred Abubakar Abdulsalam na wata kungiyar dake rajin yaki da cin hanci da rashawa da kuma kawo kyakyawan shugabanci a cikin kasa yace suna maraba da rahoton cibiyar. Satar shanu ko rikicin Boko Haram ba hujjoji ba ne da gwamnonin Zamfara da Yobe suka bayar a matsayin dalilin da basu yi aiki ba. Jihar Borno ita ce ta fi kowace jiha a arewa maso gabas fama da rikicin Boko Haram amma duk da haka rawar da gwamnan yake takawa abun yabo ne.
Jihar Yobe, daya daga cikin jihohin da rahoton ya kunsa, tace bata yadda da rahoton ba. Aji Yerima Bula Rafa kwamishanan yada labarai na jihar yace rahoton da wani ya zauna cikin ofishinsa a Legas ya rubuta maganar banza ce. Yace yaya zai san abubuwan da suke yiwa talakawa idan bai je Damaturu ba.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5