Kakakin rundunar 'yansandan jihar Gombe DSP Pajo Attajiri ya yiwa Muryar Amurka karin bayani akan yadda wasu 'yanbindiga suka kashe 'yansanda uku tare da wasu.
Yace 'yanbindigan sun shigo masu ne sai yaransu suka samesu kafin su aikata wata ta'asa saboda 'yansandan sun tunkaresu lamarin da ya sa basu iya daukan komi ba. Cikin gumurzun da suka shiga yi 'yanbindigan sun harbe masu yara su ma sun harbi 'yanbindigan amma sun arce da raunuka.
Yanzu rundunar tana gayaw jama'a musamman asibitoci ta su sanarda su idan wasu sun zo neman jinya da rauni da suka sabu daga harbin bindiga. Yanzu dai suna kan bincike kuma idan sun gama kakakin yace zasu nemi 'yan jarida su yi masu bayani.
DSP Attajiri ya tabbatar da an kashe masu 'yansanda uku da wani farin hula daya. Sun rasa mutanen uku ne sanadiyar musayar wuta da suka yi. Duk da jikatar 'yanbindigan basu samu sun daoki komi ba.
Kakakin ya roki jama'a da su shaidawa 'yansanda duk abun da suka gani amma basu gane ba ko kuma wata fuska da basu saba ganinta ba.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5