‘Yan siyasar dai na nuna cewa, babbar matsalar da ta sa gwamnatin Najeriya ta shugaba Buhari ba ta tabuka abun kirki, shi ne rashin samun masu bin diddigin ayyukan da ta ke yi da nuna inda a ke samun zamba cikin aminci.
A taron ‘yan siyasar da ke magana ba a madadin wata jam’iyya ba a Abuja, sun zayyana lamuran da dama da su ka ce shiru da masu zabe ke yi ne ya sa ‘yan siyasar ware kafa ko daura sirdin doki su na sukuwa kan talakawa.
“Najeriya na cikin mummunan yanayi kuma iya gaskiyar maganar ke nan domin ba wadataccen zuba ido kan ayyukan da gwamnati ke yi” inji daya daga shugabannin kungiyar sa idon Farfesa Pat Utomi.
Utomi ya kara da cewa a takaice dai mutane kan tsaya zabe a Najeriya don su maida kasar tamkar shagon su, shi ya sa gwamnati a Najeriya ba ta aiki don biyan muradun ‘yan Najeriya, hakika ya dace wannan ya tsaya hakanan.
Hakanan shi ma shugaban jam’iyyar NCP ta marigayi Gani Fawehinmi, wato Yunusa Tanko ya tuno yadda ‘yan adawa su ka yi gwagwarmaya har su ka kawar da gwamnatin PDP a 2015 bayan ta yi mulkin da ba a gamsu na tsawon shekaru 16.
Shi ma tsohon Ministan matasa da wasanni Solomon Dalung ya halarci taron ya na mai cewa ya dace kowa ya sa hannu don ceto Najeriya.
Gwamnati mai ci ko a ce shugaba Buhari zai kammala wa’adin mulkin sa a ranar 29 na Mayun 2023 kuma duk in ya samu dama ya kan ce ba zai nemi tazarce karo na uku ba.
Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-Hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5