Tun ranar da rahotanni suka bayyana akan cewa ana cinikin bayi a kasar Libya, shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya nuna kaduwa da faruwar wannan al’amari inda ya bukaci kotun bin kadin mayan lafuka ta duniya ta ICC da ta gaggauta gudanar da bincike domin hukunta masu aikata wannan danyen aikin.
Sai dai masu rajin kare hakkokin Bil’adama irinsu Ali Buzu na kungiyar da ke yaki da bauta na ganin maido da ‘yan Nijar kasarsu shine abin yi don tsirar da su daga wannan ukubar. A cewarsa, ofisoshin jakadancin wasu kasashen kamar su Ghana da Najeriya da sauransu na kokarin fito da ‘yan kasarsu, don haka ya kamata gwamnatin Nijar ta tashi tsaye don neman hanyar da za a ceto ‘yan kasar.
“Yanayin rashin tsayayyar gwamnati a Libya na kawo cikas wajen kokarin dawo da ‘yan Nijar” a cewar Son Allah Dambaji na kungiyar Kadet.
Tun a farkon watan da ya gabata ne kungiyar matasan lauyoyin Afrika suka yi wani taro a birnin Yammai ta gargadi shugabannin kasashen Afirka akan su yi hattara game da batun ‘yancin bakin haure, dalilin da ya sa kungiyar lauyoyin ta lashi takobin gurfanar da wadanda ke da hannu a harkar sayar da bayi.
Sakataren zartarwar kungiyar matasan lauyoyin Afrika, yace ya kamata gwamnatin Nijar ta dauki matakin sanin mutanen da kuma maido da su kasarsu. Ya kara da cewa kungiyarsu ta lashi takobin gurfanar da masu hannu a wannan haramtacciyar sana’ar gaban kuliya.
Rashin gudanar da mulki na gari musamman fatali da batutuwan yaki da talauci da rashin tanadin hanyoyin samarwa matasa ilimi, na daga cikin matsalolin dake jefa nahiyar Afrika cikin halin yake-yake, lamarin da ta wani bangare ke sa matasa zuwa yawon cirani ido rufe.
Ga karin bayani cikin sauti daga Sule Mumuni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5