Yanzu dai samari da ‘yan mata ba zasu iya shan tabar shisha ba a fadarsu ko majalisarsu, wuraren da suke zuwa yin hira, suke kuma shan tabar saboda hukumomin Maradi da Agadez sun haramta shan tabar. Haka ma hukumomin sun hana matasan zuwa inda suke shagalinsu ko cin karensu babu babbaka.
Alhaji Zakari Umaru, gwamnan jihar Maradi ya fada cewa ya sa hannu kan kudurin ko dokar hana shan wannan tabar ta shisha akan tituna, da filaye da wurin shakatawar matasan.
Ya kara da cewa an ba jami’an tsaro ikon damke duk dan makarantar da aka samu a wuraren da ake yin aikin asha. Samari da ‘yan matan da aka kama sai iyayensu sun zo sun gansu a kuma gaya masu inda aka kamo dansu da ‘yarsu da kuma abun da su keyi.
Gwamnan ya ce sun dauki mataki ne domin su tsira da mutuncinsu da mutuncin garinsu da jihar gaba daya. A cewarsa idan matasa suka lalace to kasar ma ta lalace ke nan.
Bangaren matasan sun nuna gamsuwarsu game da matakan da hukumomi suka dauka kamar yadda shugaban majalisar matasa na jihar Maradi, Malam Bubakar Maimusa, ya fada.Yace sun ji dadin matakin saboda kuka suka kaiwa gwamnan jihar bayan da suka wayar da kan matasan akan illar tabar.
Shi ma magajin garin Birnin Agadez ya dauki mataki makamancin wanda gwamnan Maradi ya dauka. Ibrahim Musa, wani matashi a garin Agadez din yace matakin yayi daidai.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani
Facebook Forum