Wasu 'Yan Najeriya Sun Bayyana Fatansu Ga Sabon Shugaban Amurka

Sabon shugaban Amurka Donald Trump da Uwargidansa Melania

Ranar Juma'ar da ta gabata aka rantsar da Mr. Donald John Trump a matsayin shugaban Amurka na arba'in da biyar

Muryar Amurka ta zagaya babban birnin jihar Oyo domin jin ra'ayoyin jama'ar birnin akan sabon shugaban Amurka da kuma fatansu gareshi.

Malam Aliyu Gwadabe yace yanzu da yake ya zama shugaban kasa ya dauki kowa nashi ne kana ya taimakawa kasashen Afirka, musamman wadanda suke tasowa yanzu. Indan ba'a taimaka masu ba ba za'a samu cigaba ba, injishi. Ya kira ya so kasashen Afirka da Asiya.

Alhaji Yaro Usman ya roki Donald Trump da Allah ya rike kowa saboda injishi basa son tashin hankali. Ya rokeshi ya taimakawa Najeriya da harkokin tsaro domin a yanzu kam kasar bata da tsaro. Yace alamura sun tabarbare.

Wasu kuma suka ce shawara zasu bashi da ya gyara duniya domin su ji dadi. Yana son a samu kudi da komi da komi a Najeriya saboda kowa ya ji dadi..

Akan barazanar da Donald Trump yayi na korar baki lokacin da yake neman zabe wani dan taliki cewa yayi ya sassauta kana ya kira shugaban ya dubi kasashen Afirka da idon rahama.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu 'Yan Najeriya Sun Bayyana Fatansu Ga Sabon Shugaban Amurka - 2' 59"