Donald Trump zai ziyarci cibiyar leken asiri yau Asabar, yau shine kwanansa na farko a matsayin shugaban kasa, daya daga cikin cibiyoyin leken asirin da ya yi ta samun sabani dasu a lokutun baya.
A baya dai Trump ya sha kushe aikin cibiyar leken asiri ta CIA da sauran cibiyoyin leken asiri, domin matsayinsu kan kutsen da suka hakikanta cewa, Rasha tayi a lokacin zaben Amurka. A kwanakin baya, Trump ya zargi hukumar CIA da kwarmata wadansu bayanan da aka ce zasu rage masa kima, da ake zargin cewa Rasha ta tattara.
Kafin ya ziyarci hukumar CIA, Trump zai yi addu’a a majalisar National Cathedral tare da iyalansa da mataimakinsa Mike Pence da kuma mai dakin Pence Karen.