Wasu 'Yan Majalisar Dattawa Na Zawarci Sanata Ndume

Sanata Muhammad Ali Ndume

Majalisar dattawan Najeriya na bukatar Sanata Ali Ndume ya nemi gafara kafin a maida shi

Makonni biyu da suka wuce ne Majalisar Dattawan Najeriya ta dakatar da Sanata Muhammad Ali Ndume na tsawon watanni shida lamarin da ya sa sarakunan Borno da dattawan jihar suka nufi Abuja domin neman masalaha kana dubun dubatan mutane daga mazabarsa suka shiga yin zanga zangar kin jini abun da aka yi mashi.

Bisa dakatar dashi da Majalisar Dattawan tayi Sanata Muhammad Ali Ndume yace yanzu haka wasu 'ya'yan Majalisar suna zawarcinsa domin sasanta takaddamar da ta kunno kai tsakaninsa da sauran takwarorinsa.

Sanata Ndume ya bayyana hakan ne lokacin da yake zaga wasu kananan hukumomin kudancin Borno domin nuna godiyarsa bisa ga goyon bayan da suka bashi tun lokacin da Majalisar ta dakatar dashi.

Yace shi ya san babu wani laifi da ya aikata kuma har yanzu Majalisar bata bayyana masa laifin da ya aikata ba saboda haka babu wani dalilin da zai sa ya mika kansa na sasantawa da wani dan Majalisa..

Inji Sanata Ndume 'yan Majalisar Dattawa 109 ne kawai. Amma adadain 'yan Najeriya ya tasar ma miliyan dari biyu kuma mafi yawansu talakawa ne wadanda kuma suke nuna goyon bayansu ga Shugaba Muhammad Buhari. Saboda haka shi ma yana tare da al'ummar Najeriya mafiya rinjaye.

Yace dakatar dashi wata dama ce ta zama cikin jama'arsa kuma hakan zai yi. Ya bada tabbacin cigaba da fadin gaskiya komi dacinta tare da aikata gaskiya.

Sanata Ndume yace bayan kananan hukumomi tara sun yi zanga zangar nuna goyon bayansu gareshi sai Majalisar Dattawan tace sai ya fito fili ya nemi gafara kana su mayar dashi. Yace shi ba zai nemi gafara ba domin shi ya san bai yi laifi ba. Yace laifinsa shi ne goyon bayan shugaban kasa Muhammad Buri da ya keyi.

Wasu daga cikin mazabar kudancin Borno sun bayyana farin cikinsu da shi Sanata Ndume daga bisani kuma suka ce basu ji dadin yadda aka dakatar dashi ba domin shi ne yake taimakonsu.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu 'Yan Majalisar Dattawa Na Zawarci Na - Sanata Ndume - 3' 40"