Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, daga jihar Taraba ya yi tsokacin cewa akwai wadanda suka je Kotu, suka yi karar shugaban majalisar dattawa, da mataimakinsa kuma anyi adawa akansu amma ba a dakatar da su daga aiki kokuma ja masu kunne ba, dan haka batun Sanata Ndume, ba za a ce majalisa bata yi dai dai ba amma ya kamata a sake duba yadda aka gudanar da lamarin.
Sanata Yusuf, ya kara da cewa dakatar da Sanatan daga aiki tamkar dakatar da ayyuka a mazabarsa ne kuma hakan bai da ce ba domin ba mutanen mazabar ne suka yi laifi ba.
Dakatar da Sanatan ya biyo bayan rashin mutumci ne da majalisar ta yi korafin cewa yayi a lokacin da ya bukaci a yi bincike. Ko hakan ya zama laifi ne? tambayar da wakiliyar sashen Hausa na muryar Amurka, Medina Dauda Kenan ta yi wa Sanata Bala Ibn Na Allah, wanda ya mayar da martanin cewa duk abinda ya shafi majalisa, lamari ne da ya shafi kowa, dan haka jan hankalin majalisa ta yi la’akari da abinda jama’a ke cawa bai kamata ya kasnce laifi ba.
Kwararre a fannin kundin tsarin mulki Bar, Mainasa Kogo Ibrahim, ya bayyana cewa akwai sashi na 6, na bangaren shari’u ko al’kalai ko kuma kuliya, inda za a iya kai duk wani karafin da mutum ke ganin an yi masa karan tsaye ko cin mutumci, dan haka Sanata Ndume na da hurumin kai karar majalisar dattawa domin a bi masa hakkin sa.
Sanata Ali Ndume, ya shiga halin rashin jituwa da takun saka tsakaninsa da sauran takwarorinsa na majalisa ne a lokacin da ya nuna goyon bayansa ga mukaddshin hukumar EFCC Ibrahim Magu,
Ga Medina Dauda da cikakken bayani.
Facebook Forum