Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa birnin Maiduguri dake jihar Borno bayan dawowarsa daga taron kolin kungiyar hadin kan Afrika da ake kira AU a takaice, wanda aka yi a kasar Habasha. Shugaban ya kai wannan ziyarar ne don jajantawa al’ummar jihar biyo bayan wani mummunan hari da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a garin Auno wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 30 da kuma kone konen motoci da gidaje.
A lokacin da ya sauka a jihar Borno kai tsaye da birnin Addis Ababa, Shugaba Buhari ya je fadar mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Dr. Abubakar Umar Garbai domin yi masa ta’aziyyar rasuwar yayarsa, daga nan ya wuce fadar gwamnatin jihar Borno inda ya gana da gwamnan jihar Alhaji Babagana Umara Zullum da sauran mukarrabansa.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu al’ummar jihar basu yi farin cikin ziyarar shugaban ba, saboda babu wata annashuwa a fuskokin su, yawancin jama'ar birnin ma sai dai suka ci gaba da hidimominsu na yau da kullum.
Haka zalika wasu dalibai da suke wuce wa sun nuna bacin ransu har su ka yi ta fadin “Ba ma so, ba ma so” da karfi a lokacin ziyarar ta shugaba Buhari, saboda a ganin su bai cika alkawarin kawo karshen kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram da yayi musu ba a lokacin yakin neman zabensa.
Wannan dai ba shi ne karon farko da jama'ar jihar suke yiwa shugaban Najeriya iho ba, ko a lokacin da tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya kai wata ziyarar aiki shi ma sun yi ma shi ihu.
Ga rahoto cikin sauti daga jihar Borno, Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5