Gungun wasu ‘yan jarida dauke da kwalaye sun saka bakaken ledoji a fuskokinsu, sun yi zanga zanga a jihar Geogia ta kasar Amurka, domin nuna rashin amincewarsu akan sacewa da garkame wani dan jaridar kasar Afganistan me suna Mukhtari.
Lauyan Mukhtari, ya bayyana cewa an sace dan jaridar mai zaman kansa ne daga jihar Geogia, inda aka tafi da shi Azerbaijan.
Lauyan ya bayyana cewa wadanda suka sace Mukhtar na sanye ne da kaya irin na jami’an ‘yan sandan Giogia, lauyan ya kuma yi ikirarin cewa an sa tukwicin kudi Euro dubu goma akan duk wanda ya sace shi da kuma ketara iyakar kasar Amurka da shi ta barauniyar hanya ya kuma kai Mukhtari.
Gwamnatin Amurka da hukumomin tarayyar Turai da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa sun bukaci shugabannin jihar Giogia su gudanar da bincike a kan lamarin.