WASHINGTON D.C —
A wannan makon ne ministan kimiya da fasaha na Najeriya Dr Ogbonnaya Onu, ya ce gwamnatin kasar na duba yiwuwar fara koyar da darusan lissafi dana kimiyya da fasaha da harsunan kasar domin inganta ilimin kimiyya da fasa a Najeriya.
Matakin inji ministan zai taimakawa dalibai da dama a kasar cigaba kamar yarda aka ake yi a wasu kasashe Irinsu Indiya da China da Iran da Koriya.
tuni dai gwamnati ta kafa kwamitin dai-daita sahun wannan shiri, kamar yadda wakilin sashen Hausa na muryar Amurka, na Legas Babangida Jibrin ya ji ta bakin masana da malamai akan wannan mataki na gwamnati
Saurari cikakken rahoton a nan.
Facebook Forum