Wasu 'Yan-Ina Da Kisa Sun yi Sanadin Mutuwar Mutane 5

Wasu matasa zauna gari banza sun tare hanyar zuwa garin Jalingo daga Numan, inda suka kashe mutane biyar.

Wasu 'yan-ina da kisa sun datse babbar hanyar Numan zuwa Jalingo, a yankin Bali, inda suka tare wata babbar mota, kuma kafin kace kwabo suka farma wadanda ke cikin motar wadanda 'yan ci rani ne da ke kan hanyar zuwa Taraba, kuma bayanai na cewa mutane biyar aka kashe, baya ga wadanda aka raunata da yanzu haka aka kwaso su zuwa asibitin garin Numan, inda ake duba lafiyarsu.

Rundunar 'yan sandan jihar Adamawan, a ta bakin kakakin rundunar, SP Othman Abubakar, ta tabbatar da lamarin. Ya ce ba wannan ne karon farko ba, da akan tare wannan hanyar.

Lamarin da ya sa masu ababen hawa da kuma 'yan sufuri kokawa, ganin irin kisan gillar da ke faruwa a hanyar, kamar yadda wannan dan kungiyar sufuri, da ya nemi a sakaya sunansa, ke cewa.

Jami'an tsaro na cigaba da fadada bincike don gano dalilan abkuwar hakan da kuma hanyar da za a bi don magance matsalar.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu 'Yan-Ina Da Kisa Sun yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 5 2'30"