Su dai wadannan yan gudun hijira da tashe tashen hankula ya raba su da gidajensu yanzu haka sun shafe makwanni a Jalingo a sansanonin wucin gadi,inda suke kokawa game da halin da suke ciki,musamman ta fuskacin cimaka,ga kuma zargin da suke yi na cewa an maida su saniyar ware.
Yan gudun hijiran dai sun ce in baicin taimako da suka samu daga wasu kungiyoyin sakai na kasa da kasa ba wani tallafi da suka samu daga bangaren gwamnatin jihar Taraban.
Yayinda suke yabawa kunyiyoyin kasa da kasa da ke kawo masu tallafi, sun kira gwamnati ta taimaka masu. Wata ta ce ta samu shinkafa da bokiti da dai sauran kayan da za su taimaketa.
Mr James Gwani shine mataimakin shugaban 'yan gudun hijira da ke anguwan Abuja Phase II,ya bayyana halin da suma suke ciki. A cewarsa gwamnatin jihar ba ta dauki wani matakin taimaka masu ba sai dai kungiyoyin da ke tabukawa
Shugabar kungiyar dakile kissan gilla a jihar Taraba Hajiya Aisha Bashir Ardo na cikin masu taimakawa 'yan gudun hijiran a yanzu, ta bayyana kokarin da suke yi. Ta kira a taimakawa wadanda suka bar gidajensu domin su sake gina muhallansu. Ta ce kawo yanzu suna da 'yan gudun hijira sama da dubu 18. Idan an taimaka masu da kayan gini wasu za su iya komawa su ci gaba da rayuwarsu. Daga karshe ta kira hadin kai tsakanin gwamnati da kungiyoyin dake kawo taimako.
To ko me hukumomin jihar Taraban ke cewa ne game da zargin shakulatin bangaro da yan gudun hijiran ke yi a yanzu? Mr Nuvalga Danagbo shine shugaban hukumar kai dauki ta jihar ,SEMA, ya bayyana kokarin da su keyi. Ya ce ba su yi watsi da su ba domin suna kai masu abinci tare da lura da lafiyarsu. Amma yanzu suna jiran gwamnati ta ba su kudi su sake ma 'yan gudun hijiran matsuguni.
A saurari rahoton Ibrahim Abdilaziz domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5
A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz