Wasu 'yan bindiga sun kashe magajiyar garin birnin mexico

Gisela Mota yayinda aka rantsar da ita ranar Jan. 1, 2016.

An halaka Magajiyar Garin birnin Mexico, a karshen makon da ya gabata, kasa da sa’oi 24 bayan da aka rantsar da ita.

Wasu ‘yan bindiga ne suka kashe Gisela Mota, wacce tsohuwar ‘yar majalisar tarayya ce. An kuma kashe ta ne a gidanta da ke Temixco.

Rahotanni sun ce an cafke mutane uku da ake zargi da kai wannan hari, ciki har da wani mai kananan shekaru, sannan an kashe wasu mutane biyu da ake zargi a wata arangama da aka yi da ‘yan sanda.

Jaridar Los Angeles Times, ta ruwaito cewa an biya ‘yan bindigar dala dubu 29,000 domin su halaka Mota, ana kuma kyautata zaton gungun masu safarar kwayoyin nan da ake kira The Reds ne suka biya wadannan kudade.

A wata sanarwa da jam’iyyar Democrat Revolution Party ta fitar, ta nuna cewa Mota, mata ce mai karfin hali, wacce jim kadan bayan da aka rantsar da it ta bayyana cewa, za ta tunkari masu aikata miyagun laifuka kai tsaye ba tare da tsoro ba.

Wata kungiyar gamayyar hukumomin Mexico ta bayyana a shafinta na twitter cewa, an kashe ma’aikatan hukumomin gwamnati dubu daya tun daga shekarar 2006 zuwa yau a kasar ta Mexico.