Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MEXICO: 'Yan Jarida Sun Fantsama Zanga-zangar Takaicin Kashe Takwaransu


'Yan jarida rike da hoton wanda aka kashe suna zanga zanga
'Yan jarida rike da hoton wanda aka kashe suna zanga zanga

Daruruwan 'yan jarida suka shiga yin zanga zanga saboda nuna takaicin kashe dan'uwansu a kasar Mexico

Daruruwan yan jarida ne suka yi maci domin zanga-zanga nuna takaicin su na kashe wani dan jarida mai daukar hoto shi da wasu mata 4.

Wadannan yan jaridan dai suna dauke ne da kwalaye da akayi wa rubuce-ruce dake bayyana kyamar su ga irin yadda yi wa yan yan jarida, suna kira da ayiadalci tare da kawo karshen wannan lamari.

Su dai wadannan yan jaridar suna dauke dauke da hoton Rueben Espinosa, wanda ya sai da kwanaki ya tsere zuwa birnin Mexico har na tsawon makonni domi yawan barazanar da ake yi wa rayuwar sa a garin su na Veracruz.

Sai dai mai ganbatar da kara na birnin Mexico ya shaidawa manema labarai cewa an bude duk wasu hanyoyin bincikn musabbabin mutuwar Espinosa, wanda aka ceya shigo birni ne domin neman aiki.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG