Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin jihar ke kokarin kiran wannan babban taro na masu ruwa da tsaki, don lalubo hanyar magance tashe tashen hankula dake da nasaba da fadan kabilanci.
A cewar wasu shedun gani da Ido wasu maharan dauke da makamai suka yi dirar mikiya a yankin Sarkin Noma dake gundumar Damfar na karamar hukumar Ibi a Kudancin jihar Taraba. Ina aka sami asarar rayuka ciki ma harda mace da kuma kananan yara.
Shi dai yankin Ibi na daga cikin yankunan dake fama da tashe tashen hankula a jihar Taraba, da sautari kan yi nasaba da fadan kabilanci ko na addini. Sai dai wasu da abin ya shafa sunce maharan sun kai hari inda suka kashe mutane 6 mace da ‘ya ‘yan ta da mijin ta suka kuma konesu kurmus.
Yanzu haka dai rundunar yan sandan jihar Taraba ta tura karin jami’anta kamar yadda kakakin rundunar ya shaidawa wakilin Muryar Amurka ta wayar talho, don a gudanar da bincike don gano wandanda ke da hannu a wannan lamari, kuma wannan mako na zuwa ne yayinda gwamnan jihar Darius Dickson Ishaku, ke gabatar da wani taro na samun zaman lafiya a jihar.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5