Wasu 'Yan Bindiga Sun Kai Hari A Birnin Kabul

Health workers retrieve a body after an attack that targeted a bus carrying mostly government employees in Kabul, Afghanistan, June 3, 2019.

A jiya Litinin wasu maza biyar dauke da makamai su ka kai wani mummunan hari da wata mota mai shake da bama-bamai sannan suka shiga barin wuta da bindigogin su a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan, inda suka hallaka akalla mutum guda baya ga wasu da dama da su ka raunata.

Jami'ai sun ce fafatawar da ta biyo baya ba ta kawo karshe ba har sai bayan sa'o'i tara kafin jami'an tsaron Afghanistan su ka yi nasarar kashe dukkannin maharan.

Ministan harkokin cikin gidan Afghanistan Nasrat Rahimi ya ce jami'an tsaron kasar na kokarin warware bamabaman da yan ta’addan suka kawo wajen. Sun kuma yi alkawarin bayyana adadin mutane da wannan farmaki ya shafa.

Tun da farko, wani babban dan jaridar Afghanistan, Bilal Sarwary, wanda ya samo bayanai daga jami'an leken asirin Afghanistan da 'yan sanda da jami'an gwamnati, na cewa akalla mutane 40 aka kashe dayawansu sojoji ne. Amma dai jami’an gwamnatin kasar ba su tabbatar da hakan ba.