Duk da cewa wasu sun sayar da katunan zabensu akwai wasu da suka ce komenene ya faru ba zasu sayar da nasu ba.
Wasu 'yan Najeriya mazauna jihar Oyo sun bayyana ra'ayoyinsu akan zaben. Wani yace shi ya sayar da katin zabensa saboda wai shi bai san anfanin siyasar Najeriya ba. Tun lokacin da suka fara yin zabe a kasar babu wanda ya zo ya basu ko nera goma su ci abinci. Ya sayar da katin akan nera dubu biyar. Da aka ce masa yin hakan tamkar sayar da 'yancinsa ne sai yace 'yancinsa shi ne dawar da ya saya ya kai gidansa.
Wanda ya sayar da nashi akan kudi nera dubu uku yace lallura garai kuma biyan bukatansa da kudin ya fi masa katin domin babu wanda ya taba taimaka masa da ko kwandala.
Yayinda wasu suke sayar da katunansu wasu kuwa basu sami katin ba duk da wai sun sha zuwa wurin da ake bayaswa. Kodayaushe suka je sai a ce su dawo wanshekare.
Akwai wadanda suka tsere daga tashin hankalin jihar Adamawa suna nan a jihar Oyo. Irinsu babu yadda zasu yi zabe duk da rajistan da suka yi a jiharsu ta asali.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5